Republicans A Majalisun Dokokin Amurka Sun Dauki Matakin Farko Na Rusa Obamacare.

'Yan Republican zasu rusa dokar inshoran kiwon lafiya da Obama ya kafa.

Wakilan majalisar tarayya sune suka dauki mataki na baya bayan nan.

Majalisun dokokin Amurka sun amince da matakin farko na wargaza ko rusa dokar kiwon lafiya, wacce ta kasance gagarumar nasarar da shugaba Obama ya samu a tsawon mulkinsa.

A majalisar wakilai 'yan jamiyyar Republican sun kada kuri'a kan kudurin kasafin kudi da ya umarci kwamitoci su tsara doka wacce zata rusa shirin kiwon lafiyan nan da 27 ga watan nan.

A ranar Alhamis majalisar dattijai ta amince da wannan kuduri,kan dokar kiwon lafiyar da aka fi sani da inkiyarta ta Obamacare. Wannan hanyar ce mafita ga 'yan Republican a majalisar dattijai saboda ana bukatar kuri'u 60 domin hana yiwa kudurin dungu, ganin senatoci 'yan Republican 52 ne a majalisar.

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, majalisar wakilai ta kada kuri'a fiyeda sau 60 da zummar wargaza dokar,amma sun san cewa shugaba Obama ba zai amince ya sa hanu akan dokar ba.

Amma shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump yayi yakin neman zabe bisa alkawarin zai rusa dokar a maye ta da wata. Amma 'yan jam'iyyar ta Republican har yanzu basu gabatar da dokar da zata maye gurbin ta Obaman ba.