Rediyo Na Taka Rawa Wajen Neman Hadin Kan Kasa - Inji Zaidu Bala

REDIYO

Taken ranar karrama kafar sadarwa ta Rediyo na bana na da zummar “yada hadin kai a tsakanin al'umma masu al'adu da addinai daban-daban a duniya."

Hukumar raya ilimi da al'adu ta majalisar dinkin duniya da ake kira UNESCO ce ta bullo da wannan ranar da aka fara tsarawa a shekarar 1946. Bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a shekarar 2011, a shekarar 2013 aka ayyana ranar 13 ga Fabarairu a matsayin ranar karrama Rediyo ta duniya.

Duk da bullowar kafafen sadarwar na zamani na yanar gizo, har yanzu Rediyo ne ke isar da sakonni zuwa kowanne lungu da sako, a birane da karkara a fadin duniya saboda kafar ba ta bukatar wutar lantarki wajen cin gajiyar ta.

Aisha Zakari Yasmin, mai sharhi kan tattalin arziki da al'adu, ta ce mutum yakan samu natsuwar hankali wajen sauraron Rediyo ba kamar talabijin ba da zai raba hankali tsakanin sauraro da kallo.

Shi ma Adamu Attahiru, mai yada labarai ta kafar sada zumunta ya ce duk abin da a ka yi don mutunta Rediyo ba zai wuce gona da iri ba.

Jagoran kungiyar Muryar Talaka a Najeriya da ke da membobi a duk fadin kasar Zaidu Bala Kofa Sabuwa, ya ce ba za a samu nasarar hadin kan kasa ba in ba tare da tasirin kafar sadarwar Rediyo ba.

Hakika an samu gidajen Rediyo a kusan kowanne yanki da suka hada da na gwamnati da kuma masu zaman kansu, inda bambancin aikin ya shafi masu tsage gaskiya, masu ririta ko boye gaskiyar da masu yada abin da masu mulki ke so.

Kafafen yada labarai na kasa-da-kasa na samun tagomashin aiki ba tare da katsalandan ba.

A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Rediyo Na Taka Rawa Wajen Neman Hadin Kan Kasa - Inji Zaidu Bala