Real Madrid Na Samu Koma Baya Tun Bayan Tafiyar Ronaldo

Dan wasan kungiyar Real Madrid Luka Modric

Dan wasan Real Madrid mai rike da kambun gwarzon tamola a duniya, Luka
Modric, ya ce har yanzu ‘yan wasan gaba na kungiyar sun kasa cike gibin da Cristiano Ronaldo ya bari.

Dan wasan dan kasar Crotial ya bayyana koken ne, yayin da suke shirin tunkarar fafatawarsu da Ajax yau Talata, a gasar zakarun turai, inda za su karbi bakuncin kungiyar a Santiago Bernabeau wasan zagaye na biyu.

A karawarsu ta farko dai Real Madrid ce ta yi nasara da kwallaye 2-1 akan Ajax. Gwarzon dan wasan ya ce tun bayan rabuwar kulob da dan wasan Cristiano Ronaldo da ya koma Juventus, Real Madrid ta gaza ci gaba da nuna kwazo, a fagen yawan zura kwallaye da kuma samun nasarori kamar yadda takeyi a baya.

Real Madrid ta sayi ‘yan wasa masu kananan shekaru da suka hada da Vinicius Junior da Mariano Diaz, tun bayan da ta sayar da Ronaldo sai dai babu wani shahararren dan wasa da ta sayo domin maye gurbin na Ronaldo.

A tsawon kusan shekaru 10 da Ronaldo ya shafe tare da Real Madrid, ya zura mata kwallaye 451, a wasanni 438 da ya buga mata sai dai bayan tafiyarsa Juvenus da kuma ajiye aiki da tsohon kocinsu Zinaden Zidane yayi, kungiyar ta soma fuskantar matsaloli.