Real Madrid Ba Ta Shirin Sayen Wani Dan Wasa

Zinedine Zidane

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane, ya karyata rade radin da ake yi na cewar, kulob din na fama da rashin dan wasan gaba, kuma za ta sayo dan wasan gaba a watan Janairun 2020, da zarar an bude hada hadar saye da sayarwa.

Zidane ya bayyana hakan ne jimkadan bayan tashi daga wasan da su ka yi kunnen doki 0-0 tsakaninsu da Athletico Bilbao a gasar Laligar bana.

A lokacin da 'yan jarida su ka tambaye shi ko Real Madrid tana da bukatar sayen dan wasan gaba a watan na Janairu? sai Zidane ya kada baki ya ce sam, babu wani bukatar hakan da gaggawa kamar yadda jama'a suke nufi.

Madrid dai ta na da manyan 'yan wasan gaba da su ka fafata a wasansu da Bilbao, sun hada da Karim Benzema, Rodrygo Silva De Goes, da kuma Vinicius Jose Junior.

Kungiyar ta jera wasanni biyu kenan a bangaren Laliga a satin da ya gabata, ba tare da ta jefa kwallo ba, inda suka tashi canjaras da babbar abokiyar hammayarta Barcelona a Camp Nou.

Kuma ta na mataki na biyu ne da maki 37 a teburin Laligar bana, wasan mako na 18, banbancin maki biyu tsakanin ta da Barcelona wacce ta ke saman teburin.