Ba abin mamaki ba ne dan Najeriya nan da ya murzawa kasar leda, a gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekara 17 Peter Olawale, wanda ake wa lakabi da dan karamin Ronaldo, ya shiga manyan kungiyoyin duniya.
Ana dai sa ran dan wasan ya shiga daya daga cikin manyan kungiyoyi da suka hada da Greither Furth, Real Madrid ko Borussia Dortmun.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan rawar da ya taka a gasar cikin kofin duniya na shekarar 2019.
Matashin mai shekaru 17 wanda ke tsaron gida, ya taka rawar gani a wasan da suka buga da Netherlands, a zagaye na 16.
Kuzarin matashin wani abin dubawa ne da kuma yadda yake bin kwallo, idan aka lura da irin rawar da ya yi lokacin wasansu da Australia wanda aka tashi da ci 2-1.
Wakilan kungiyoyi daga kasashen Andalus, da Jamus sun halarci wasan don duba hazakar matashi Olawale, da aka yi a kasar Brazil, kana suna kuma ci gaba da ganawa da manajojin matashin a birnin Ibadan da ke jihar Oyo don ganin yadda za su saye shi.
Majansa Olatunji Samuel Okuku, ya ce ya zuwa yanzu “kungiyar Greuther Furth ta kasar Jamus ta rubuto a hukumance cewar suna son sayan dan wasan, da fatar za su kada dayan kugiyar da ke kokarin sayan shi ta Blancos da Die Borussen.“
Akawai dai kungiyoyi da dama da suke kokarin sayen dan wasan a cewar manajan Olawale.