Rawar Ungo Zoma a Lokacin Juna Biyu da Haihuwa

Muhimmancin zuwa awon ciki yana da yawa.

Shin wai ya kamata ace haryanzu Ungo Zoma na karbar haihuwa kuwa? Wasu dalilai kesa har yanzu a kasashen Hausa mata Ungo Zoma, ke taka rawar gani wajen taimaka ma mata masu juna biyu.

A irin al’ada da addini a kasar Hausa mata da dama basa zuwa asibiti lokacin haihuwa bisa dalilin karancin mata masu duba su musamman ma a lokacin haihuwa, a cewar wata mata da take bayyana dalilin da yasa bata zuwa asibiti don awo da kuma haihuwa.

Watama tana ganin ai wadannan ungo zoman suma suna da kwarewa kamar wasu malaman asibiti, don haka suna ganin gara ace unguwar zoma ta taimakamu su a lokacin haihuwa da ba zaisa suje asibiti ba, a wani bangaren kuma rashin zarafi wato kudi kesa wasu mata basu zuwa asibiti don awo da haihuwa.

Tabakin Hajiya Sa’adatu Tajalli, wadda take unguwar zoma ce da ta share kimani shekaru talatin tana taimaka ma mata wajen samun sauki a lokacin haihuwa.

Ita dai Hajiya Tajalli, tace a lokutta da dama akan kirata wajen haihuwa wanda take taimakawa mata da wasu addu’o’I da kuma wasu dabaru a lokacin haihuwa wadda abun da takeyi musu mafi akasari shine akeyima mata a asibitoci, don haka tana taimakawa matuka ga mata masu haihuwa.

To abun la’akari dashi a nan shine yakamata iyaye su sa ‘yayansu mata makaranta don su samu ilimin zamani don taimakama ‘yan’uwansu mata a lokacin haihuwa da ma hali nayau da kullun. Ta haka ne kawai za’a samu al’uma mai nagarta da taimakon kai da kai.