Rawar Da Sojojin Saman Najeriya Suka Taka Akan Boko Haram

Hedkwatar Sojojin saman Najeriya, tayi Karin haske akan rawar da ta taka wajan kwato dajin Sambisa, daga hannun mayakan Boko Haram.

Tunda farko sai da Sojojin saman Najeriya, suka tayin rowan boma bomai, a duk bangarorin da mayakan Boko Haram, suke a cikin dajin Sambisa, kafin daga bisani Sojojin kasa su kutsa cikin wannan dajin.

Da yake Karin haske kan rawar da dakarunsa suka taka babban hafsan Sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadiq Abubakar, yace Sojojin saman sun tayin sintiri akai akai cikin shirin ko ta kwana domin tabbatar da sa ido da tallafawa mayakan kasa.

Masani tsaro Aliko El-Rasheed Haruon, yace an daukin Sojojin saman Najeriya, a matsayin na zamani, kuma rundunar Sojan sama tayi rawar gani domin a cewarsa akwai wuraren da yake idan sojojin sama basu kai farmaki ba Sojojin kasa bazasu iya shiga ba.

Itama rundunar Sojan ruwan Najeriya, baduka ‘yan Najeriya, bane suka san cewa ta taka rawa gaya wurin karya lagon Boko Haram, ba.

Kakakin rundunar Sojojin ruwan Najeriya, Rear Admiral Christian Ezekobe, yace rundunar Sohan ruwan Najeriya, tanada dakaru na masamman, da ake kira (SBF) masu kama da irin na kasar Amurka, wadanda ake kaisu fagen daga domin kai farmaki na masamman, kuma akwai wasu dakarun dake cikin bataliya ta Sojoji.

Your browser doesn’t support HTML5

Rawar Da Sojojin Saman Najeriya Suka Taka Akan Boko Haram - 2'45"