Yau Dandalinvoa ya sami zantawa da jarumi Ahmad Bello, wanda aka fi sani da Nazir a cikin shirin Dadin Kowa na Arewa 24, inda suka tattauna akan yadda harkokin shaye-shaye suka yi kamari a tsakanin matasa mata da maza da mata.
Ya kuma yi bayani kan irin rawar da jaruman matasa ke takawa wajen wa’azantarwa da fadakarwa akan illar wannan mummunar dabi’a.
Ahmad ya bayyana cewa matasa su ne kashin bayan kowace al’umma, amma abin takaicin shi ne, matasa su ne suka tsunduma cikin wannan mummunar dabi’a ta shaye-shaye.
Ku Duba Wannan Ma Dan Guntun Gatarin Ka - Inji Fiddausi Mai Karamar Sana'aKowacce al’umma na dogaro ne da matasa domin kuwa su ne manyan gobe, hakazalika, su ne ya kamata su kasance abin dogaro domin samun kyakkyawar makoma.
Daga cikin irin illolin da ke tattare da shaye-shaye sun hada da haifar da rashin lafiya, rashin dogaro da kai da kuma rashin cimma burinsu na rayuwa.
Ahmad ya bayyana cewa matasa jarumai na taka rawar gani wajan jawo hankalin al’umma musamman ganin yadda matasa ke kaunar kallon fina finai.
Ya kara da cewa, ta wannan hanya ce suke kokarin yin amfani da duk labarin da zai iya zama ishara ga wanda ke cikin irin wannan yanayi domin fadakar da shi.
Daga karshe ya bayyana cewa koda fim na sa'a guda ne, jarumi zai yi kokarin jefa wani abu da zai kawo gyara koda na minti guda ne wanda aka iya yin tasiri.
Your browser doesn’t support HTML5