Dantakarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump wanda a yakin neman zabensa ya bayyana cewar idan ya ci zabe zai hana musulmi shiga kasar ya aika da sakon ta'aziyyar sa ga iyalin marigayi Muhammad Ali fitaccen dan damben Boxing wanda ya rasu ranar juma'ar data gabata.
Koda shike kafin marigayin ya rasu, yayi Allaha wadai da kalaman Donald Trump na cewar zai hana musulmi shiga kasar Amurka idan ya ci zabe, lamarin da ya haifar da cece-kuce a Amurka da kuma sauran kasashen duniya.
A yanzu haka dai sakon gaisuwar da Trump ya aika ya zama abin cece-kuce a tsakanin sa da sauran takwarorin sa na jam'iyyar Democrat inda Bernie Sanders ya zargi Donald Trump da rashin iya magana da sanin inda ya sa gaba.
Muhammad Ali ya rike kanbin damben zamani boxing na duniya, daga karshe marigayin yayi fama da rashin lafiya kuma ya rasu ne a ranar juma'a data gabata a birnin Louisville dake birnin Kenturkey dake nan jahar Amurka.
Idan Allaha ya kaimu ranar Juma'a mai zuwa ne za'a yi janaizar sa kamar yadda iyalan marigayin suka bayyana.