Rasuwar Justice Mamman Nasir

Sandar Alkali

Tsohon shugaban kotunan daukaka kara a Najeriya, Justice Mamman Nasir ya rasu ne yana mai shekaru 90 da haihuwa.

Rahotanni daga masarautar jihar ta Katsina, sun bayyana cewa a jiya Asabar marigayi Mamman Nasir ya rasu, kuma tuni aka yi jana’izarsa a jiyan.

Ya rasu ne a asibitin Tarayya na Jihar Katsina.

A shekarar 1929 aka haifi tsohon shugaban kotunan na Najeriya, ya yi karatu a kwalejin da ke Kaduna inda ya kammala a shekarar 1947.

Ya kuma yi karatu a jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya.

Sannan ya yi karatu a birnin London na Burtaniya, inda a nan ne ya yi nazarci ilimin digiri a fannin shari’a.

A shekarar 1978 aka nada shi a matsayin shugaban kotunan daukaka kara, mukamin da ya rike har zuwa shekarar 1992, wato lokacin da ya yi ritaya.

A kuma shekarar ne aka nada shi a mukamin Galadiman Katsina.