Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya CNG ta bayyana alhininta game da rasuwar daya daga cikin dattawan yankin arewa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Alhaji Bashir Othman Tofa.
Gamayyar ta bayyana marigayin a matsayin wani jigo da al’umar yankin arewa ba za su taba mantawa ba.
A wani hira da ya yi da Muryar Amurka, shugaban gamayyar kungiyar, Balarabe Rufai ya bayyana jagoranci da sadaukar da kan da marigayin ya yi ga al’umar Najeriya musamman al’amuran da suka shafi yankin Arewa a matsayin abin koyi.
Balarabe ya kuma bayyana kaduwarsu game da rasuwar dan siyasar haifaffen jihar Kano, ganin yadda rayuwarsa da ayyukansa suka zama abin zaburarwa da koyi ga dimbin matasan da suka fito daga yankin.
A cewarsa, babban abin da za su yi koyi a matsayinsu na matasa shi ne tsayawa akan gaskiya, domin mutum ne mai tsoron Allah, kuma ba ya duba wani balle yaji tsaro, sannan kuma mutum ne wanda ba shi da kwadayi.
A sakamokon wannan rashi da aka yi gammayar kungiyoyin ta bayyana cewa ta jinginar da taronta da ta shirya yi a ranakun 5 da 6 ga wannan watan na Janairu kan hada masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro a wani mataki na nemo bakin zaren matsalar tsaro dake addabar yankin na arewacin Najeriya.
A safiyar yau Litinin aka sanar da rasuwar Alhaji Bashir Tofa wanda ya kasance ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban kasa a zaben 1993, zaben da ake yi wa kallon zabe mafi adalci a Najeriya. Tuni an yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Your browser doesn’t support HTML5