Na baya bayan nan ma shine cece-kucen da yanzu ake yi game da hukuncin da wata kotu ta yanke a jihar na daurin wani magidanci Mallam Abubakar, dake sana’ar fawa, da yayi yunkurin yiwa agolarsa yar shekaru shida da haihuwa fyade a anguwar Yolde Pate-Hayin Kogi, inda aka yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan yari ko kuma ya biya taran naira dubu takwas (N8000).
Kamar yadda bayanai suka tabbatar, magidancin Abubakar Mahauci, ya so yayiwa agolar da matarsa ta zo gidansa da ita fyade ne, da hakan yayi sanadiyar raunata yarinyar da yanzu haka ke ci gaba da jinyar raunin da yayi mata da hannu.
Ita dai mahaifiyar wannan yarinya da aka sakaya sunanta Malama Fatima, ta auri Mallam Abubakar ne bayan rasuwar mijinta na farko wato mahaifin wannan yarinya da aka lalata.
Kuma kawo yanzu yarinyar na cikin wani halin ban tausayi inda take tafiya da kyar.
Makwabtan wannan mutumin sun tabbatar da afkuwan lamarin tare da nuna takaici.
A karamin asibitin da aka fara duba yarinyar dake Yolde-Paten jami’in dake kula da asibitin wato in-charge, Ibrahim Tuta, ya tabbatar da raunin da aka yiwa yarinyar yar shekara shida a al-aurarta.
To sai dai yayin da yarinyar ke fama da raunin da aka yi mata, kungiyoyin kare hakkin yara na ganin akwai abin dubawa a wannan hukuncin shekaru biyun da aka yanke.
Barista Ibrahim Muhammad Gwary, wani lauya ne mai zaman kansa ya zargi jami’in yan sanda wato prosecutor da cewa shi ya barar da shari’ar a gaban alkali.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5