Rashin 'Yan Jarida A Fadin Duniya, Zai Maida Komi Baya

A cikin jawabin sa na shekara-shekara a bana ya bayyanar da irin rawar da 'yan jarida ke takawa a duniya, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, yace akwai bukatar jinjinawa 'yan jarida a fadin duniya, saboda irin rawar da suke takawa wajen wayar da kan jama'a.

Ya kara da cewar 'yan jarida na taimakawa wajen sanar da jama'a a fadin duniya halin da duniyar ke ciki, da kuma irin hanyoyi da suka kamata mutane subi don inganta rayuwarsu.

Haka zalika suma wasu mutane da suka bayyana ra'ayinsu dangane da muhimancin 'yan jarida, suna masu cewar ta kafofin yada labarai suka dogara wajen samun labarai masu sahihanci, da kuma yadda zasu tafiyar da ayyukan su na yau da kullun.

Wakilin sashen Hausa Babangida jibrin ya hada muna wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Rashin 'Yan Jarida A Fadin Duniya, Zai Maida Komi Baya 2'20"