Irin wannan al'amari na rashin tsaron ne ya faru a garin Takakume da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato, inda barayi suka afka wa jama'a, su ka tarar da su farke, aka yi bata-kashi tsakaninsu.
Lamarin rashin tsaron dai yana ci gaba da ta'azzara, inda ake ci gaba da samun hasarar rayukan jama'a a sassa daban daban na Najeriya, musamman ma dai a arewa.
Mazauna garin Takakume da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, da daren jiya asabar, sun dauki bakuncin ‘yan bindiga, wadanda suka afka, sai suka tarar da jama'a falke, daga nan suka soma musayar wuta.
Shugaban karamar hukumar ta Goronyo, Abdulwahab Yahaya Goronyo, wanda da shi ne aka yi Jana'izar mutane 7 da aka kashe a bangaren mutanen garin na Takakume, ya ce yanzu kura ta lafa a yankin.
Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriya amma dai abin ga gagara
Yan Najeriya dai na ci gaba da kira ga mahukumta da su kara azama koda za a shawo kan wannan matsalar da ta addabi jama'a.
Saurari cikakken rahoton Mohammed Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5