Rashin Tsaro Ya Hana Habakar Yawon Bude Ido A Jihohin Taraba da Adamawa

Gwamnan Jihar Taraba Darius Dickson Ishaku

Jihohin Taraba da Adamawa sun koka da koma baya da fannin yawon shakatawa da tattalin arzikinsu ke fuskanta a shekarun baya sakamakon fadan kabilanci da hare-haren Boko Haram da suka addabi yankin da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Gwamnana jihar Taraba Akitek Darius Dickson Ishaku ya bayyana haka cikin hirar da wakilin sashin Hausa Sanusi Adamu ya yi da shi kan ranar yawon shakatawa ta Majalisar Dinkin Duniya. Tattalin arzikin Jihar Taraba ya raunana ainun a ‘yan shekarun baya duk da gandun dajin Gashaka Gunti mafi fadi a nahiyar Afrika da kuma tafkin Munyo na wuraren yawon shakatawar da take alfahari da su sakamakon fadan kabilanci inji gwamnan.

A makwabciyarta jihar Adamawa wacce take da daular Sukur ta farko a nahiyar Afrika da asusun cibiyar raya al’adu na Majalisar Dikin Duniya ta kebe a 1999 da masu yawon shakatawa, masu nazarin tarihi da dalibai a bayan kan ziyarce ta sun dauke kafa shekaru uku da suka gabata.

Ciroman Sukur Saleh Kinjir kuma shugaban gidauniyar raya ayukan yawon shakatawa na Sukur mai zaman kanta ya shaidawa Muryar Amurka cewa barnar da kungiyar Boko Haram ta haddasa ta mai da hanun agogo baya a kokarin da gwamnati ke yi na daukaka matsayin ta ta yadda zata yi gogayya da sauran takwarorinta na kasashen Afirka

Sai dai kokarin da na yi domin jin matakan da gwamnatin Adamawa ke dauka na farfado ayukan yawon shakatawa Sukur ta bakin kwamishinan al’adu da raya yawon shakatawa Tawali’u Magaji Nathan musamman yanzu da ‘yan gudun hijira ke komawa gidajensu.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rashin Tsaro Ya Hana Habakar Yawon Bude Ido A Jihohin Taraba da Adamawa - 3' 27"