Rashin Sana'a Ko Aikin Yi Babbar Matsala- Inji Sakina Mohammed

Sakina Mai Gyaran Gashi

Sakina Mohammed ma’aikaciya a wani shagon gyaran gashi na tafi da gidan ka wanda suke bin kwastomomi har gida idan suna da bukatar hakan domin a yi masu aiki daidai da yadda suke bukata.

DandalinVOA dai ya iske malama Sakina cikin rigar aiki mai dauke da alamar sunan shagon da take aiki inda ta dukufa tana yi wa wata mata kunshi, a hannu guda kuma wasu suna jira ta kammala domin ta yi masu kitso.

Sakina dai ta ce tana aiki ne a wani shagon gyaran gashi mai suna Darain dake jihar Kaduna inda suke da saloon sannan suke zuwa gidajen biki ko su biyo mace gidanta domin ayi mata gyaran jiki ko gashi da sauransu.

Ta ce bayan ta koyi aiki a saloon dinne ta fara aiki a shagon, sannan ta ce babban abinda ya ja hankalinta ta fara sana’ar dogaro da kai shine a cewarta mutum babu aiki kuma bashi da anfani ya zauna babu wata sana’a shine daya daga cikin dalilan da ya sanya ta fara wannan sana’a.

Ta ce aiki ga diya mace abune mai matukar muhimmanci mussaman ma a wannan lokaci domin mace zata kashe wannan dabi’ar ta bani-bani.