Rashin Masu Saka Jari Cikas Ga Sana'ar : In Ji Kenny Wonder

Kenny Wonder

Rashin masu saka jari a harkar wake wake a Najeriya, yana jawo koma baya ga harkar in ji Kenny Wonder, wani mawaki kuma furodusa a Kannywood.

Kenny ya furta haka ne a wata hira da wakiliyar muryar Amurka Baraka Bashir, a birnin Kano, inda ya kara da cewa mafi akasarin mutane basu da yakinin cewar waka wata abace da ta ke samar da kudaden shiga.

Yana mai cewa banda matsalolin rashin goyon baya da mawaka ke fuskata da kallon rashin da’a da ake yi musu matsalar zuba jari shine babban kalubale.

Kenny Wonders ya ce wannan matsala dai ta fi yi katutu a arewancin najeriya, inda mafi yawan lokuta mawaka kan sanya kudadensu ba tare da suna da tabbacin samun abinda suka kashe ba.

Ya ce babban burinsa a yanzu shine ya bude kamfanin da zai bai wa mawaka damar shiryawa da fitar da wakokinsu amma fa a karkashin sunan kamfanin sa.

Ya ce shigarsa jihar Lagos ya kara bude masa ido da kara nisan zangon harkarsa don kuwa ya samu damar yin waka da manyan mawaka irinsu, Classic, 2Face , Olu Maintain da sauransu.

Your browser doesn’t support HTML5

Rashin Masu Saka Jari Cikas Ga Sana'ar : In Ji Kenny Wonder - 5'55"