A yau shirinmu na kananan sana'oi na mussaman ne domin kuwa mun sami bakuncin hajiya Usaina Ahmad, mataimakiyar shugaban kungiyar masu kananan sana'oi ta kasa wacce ta ce rashin isashshen jari na dakushe kananan sana’oi tare da kawo koma baya ga harkar.
Ta kara da cewa rashin isashen wutar lantarki da rashin bude kungiyoyin na sana'oi na daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga masu kananan sana'oi a wannan yanki na arewa.
Hajiya Usaina, ta ce bankuna na bada lamuni akwai bankin musulunci da ma bankuna na bada aron kudi domin a bunkasa kananan sana'oi amma babban muhimmin sai an bude wa sana'oi kamfani tare da shiga kungiyar ne za’a iya samun kudin da za’a bunkasa sana’a.
Ta ce dole ne a zamanantar da sana’a domin shiga sahun wajen gogayya da sauran masu sana’oi wajen tallata hajarsu da samun tallafi daga kungiyoyin kasashen waje da ma gwamnatin kasa.
Your browser doesn’t support HTML5