Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda a halin yanzu yake wakiltar Najeriya a taron kasashen G-20 a kasar Indiya, ya yi wata tattaunawa da ‘yan Najeriya da yammacin ranar Alhamis.
A yayin wannan taro, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa rashin ingantaccen shugabanci da gudanarwa a ma’aikatun gwamnati ne ya sanya shi tsayawa takarar shugaban kasa.
Da yake jawabi a wurin taron, shugaba Tinubu ya jaddada muhimmiyar rawar da al’adu da kabilu daban-daban na Najeriya ke takawa wajen ciyar da ci gaban kasa gaba.
Ya jaddada cewa arziƙin ƙasar na iya zama madogara mai ƙarfi don haɓakar tattalin arziƙin ƙasa, ƙirƙira, da ci gaban zamantakewa, wanda a ƙarshe zai amfanar da kowane ɗan ƙasa.
"Mun zo nan ne don gabatar muku da sabuwar makoma. Makomar kasa mai wadata, wadata, da yawan jama'a, cike da nau’i da dama, tsarin rayuwa daban daban mai ban sha’awa na daga kabilu daban daban da al’adu masu kyau, Wannan shi ne zai sa ci gabanmu ya yiwu, idan har za mu iya yin amfani da bambancin mu don samun wadata, ”in ji Shugaba Tinubu.
Da yake karin haske kan dalilansa na tsayawa takarar shugaban kasa, Tinubu ya bayyana cewa, duk da dimbin albarkatun dan Adam da na kasa, al’ummar kasar na fuskantar cikas sakamakon gazawar shugabanci da gudanar da harkokin gwamnati.
Ya tabbatar da cewa, “Mu ba matalauta ba ne a fannin ilimi, ba mu da talauci a fannin ’yan Adam, mu talakawa ne kawai wajen gudanar da mulki da shugabanci, shi ya sa na yi takarar shugaban kasa, domin in taimaka mana mu gyara ruhin kasarmu a cikin hanya madaidaiciya."
Da yake yin la'akari da gwagarmayar tarihin rayuwarsa, Shugaba Tinubu ya ƙarfafa ɗaliban Najeriya da ke karatu a Indiya don neman nasara ta hanyar sadaukarwa, gaskiya, jajircewa, da kuma canza tunani.
Ya ba da labarin yadda ya fara a rayuwarsa, tun daga matsayinsa na mai gadi, har ya zama babban akawu, babban mai binciken kudi, ma’ajin kudi, sannan kuma ya zama shugaban siyasa, inda ya jaddada cewa ingantaccen ilimi ya taka muhimmiyar rawa a cikin tafiyarsa da rayuwarsa baki daya.
"Haka kuma za ku iya; kada ku kasance masu yanke kauna ta kowace hanya. Najeriya a shirye take ta karbi kowa da kowa,kuma ta ko wane bangare na Najeriya kuke," in ji shugaban da yake tabbatar wa daliban.
A yayin taron, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi karin haske game da manufofin Shugaba Tinubu kan manufofin kasashen waje, da suka hada da inganta ayyukan ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje.
Ya yi alkawarin kawar da jinkirin fasfo, ya kuma bukaci daliban Najeriya da ke kasashen waje da su kare mutuncin kasar su wajen fitowa da kyakkyawan yanayi da halayya mai kyau.
Babban hamshakin dan kasuwa Mista Tony Elumelu shi ma ya yi jawabi ga manema labarai, inda ya bayyana amincewarsa ga Najeriya a matsayin kasar da tafi cancanta ga masu zuba hannun jari. Ya bayyana nasarorin da Najeriya ta samu a duk duniya tare da jaddada cewa zuba jari a Najeriya a yanzu zai kawo wa masu zuba hannun jarin dimbun riba mai tarin yawa mara misaltuwa.
A ƙarshe, jawabin da shugaba Tinubu ya yi a yayin taron G-20 a ƙasar Indiya, ya yi daidai da kiraye-kirayen kawo sauyi ga shugabanci da kuma amfani da albarkatu daban-daban na Nijeriya don ci gaban ƙasa. Yayin da al’ummar kasar ke fuskantar kalubale daban-daban, kalaman nasa sun zama abin tunatarwa kan irin karfin da za a samu a yayin da shugabanci ya yi daidai da dimbin arzikin kasar.
~Yusuf Aminu Yusuf