Yau ce ranar yaran Afirka wace ke dai dai da zagayowar ranar 16 ga watan yuni 1976 ranar da jami’an tsaro suka bindige wasu dalibai bakaken fatar Afirka ta kudu dake zanga zangar nuna damuwarsu da wariyar launin fatar da ake nuna masu wajen samin ilimi a makarantu.
Batun ba yara ilimi mai inganci ne shine abinda kungiyar hada kan Afirka (AU) ta sa a gaba wajen bukukuwan karrama wannan rana .
Samarda ilimi ga kowane yaro wani ‘yanci ne da kasar Nijar tayi amanna akansa dauko daga dokokin cikin gida da yarjeniyoyin kasa da kasa sanar kasar tayi Imani cewa bada ilimi mai inganci zai fi tasiri akan rayan da zasu jagoranci al’uma a gobe, sai da rashin cimma wannan buri ya shiga halin rashin tabbas saboda wasu dalilai in ji jagoran kungiyoyin CONED, masu kare hakkin yara Musa Sidikou.
A bayane ake gane irin wadannan matsaloli na koma bayan ilimi a makarantun firamari da sakadare kamar yadda Aishatou ke cewa ita ganau ce.
Ministan Al’uma Rakiyatou Christelle Jaku, na cewa koma baya ilimin yara a makarantun kasar Nijar, wani abune da ta wani bangare za a iya dangantawa da cikoson yara a ajujuwa.
Lura da yadda kowane bangare ke cigaba da cewa ya kyautu ‘yan majalisar dokoki su kira ministan ilimi ya bayana zauran majalisan domin yin bayani domin ilimi ake nema saboda idan yara basu yi karatu ba hasara ce ga Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5