Har yanzu marasa aikin yi a kasashe da suka ci gaba yana da yawan gaske, wadda yake janyowa shugabanni rashin barci, akokari da suke yi na kaucewa wata koma bayan tattalin arzikin Duniya.
Alkaluma da kungiyar ci gaban tattalin arziki da ayyukan more rayuwa ta sake ya nuna cewa rashin aikin yi a fadin kasashe 34 dake cikin kungiyar, ya haura zuwa kashi 8.3 cikin watan Oktoba, daga kashi 8.2 cikin watan Nuwamba.
Kungiyar OECD tace adadin mutane da basu da aikin yi a kasashe da suke kungiyar mutane milyan 45 da dubu dari daya cikin watan Oktoba, galibin wan nan adadi a turai ne.
Yankin turai baki daya yaga rashin aikin yi ya haura zuwa kashi 10.3,wan nan shine kashi mafi yawa da ya taba gani tun lokacin da Duniya ta fuskanci koma bayan tattalin arziki.
Kasar Spain da Netherlands su suka ga karuwar rashin masu aikin yi, Andalusiyar (Spain) ta yawan wadanda basu da aikin yi ya kai kashi 22.8. Masu fashin baki suna fargabar matsalolin tattalin arziki da Spain take fuskanta zai tilastawa kasar ta hudu a girman tattalin arziki a yankin kasashe na Euro ta shiga sahun Girka da wasu kasashe d a suka nemi tallafin kasa da kasa domin magance matsalar da suke ciki.
Haka ma a alkaluma da aka sake cikin watan Nuwamba ya nuna rashin aikin yi ya ragu a Amurka, tattalin arziki mafi girma a Duniya da kamar kashi 0.4.