Rashawa Na Daga Cikin Ababen Da Suka Jafa Najeriya Cikin Matsalar Man Fetur - Muhammad Saleh Hassan

Muhammad Saleh Hassan kwararre kan harkokin mai fetur a Najeriya

Matsalar karancin man fetur da al’ummar Najeriya ke cigaba da fuskanta na kusan makonni uku, ya kara taka rawa wajen haifar da matsin rayuwa na yau da kullum.

ABUJA, NIGERIA- Wani Ƙwararre a harkar man fetur kuma Shugaban kamfanin Skymark Energy and Power Limited a Najeriya, Alhaji Mohammed Saleh Hasan ya bayyana wa muryar Amurka cewa daga cikin dalilan da suka taimaka wajen haifar da matsalar karancin mai da Kasar ke fuskanta akwai batun wasu daga cikin dilalan mai na kasar da suka karbi cin hanci da rashawa wajen shigar da gurbataccen man da ya rinka lalata ababen hawa na al’umma.

Toh sai dai a cewarsa tuni shugaban Kamfanin NNPC Mele Kyari ya daura dammara wajen daukar matakai na janye gurbataccen man da aka shigo da shi tare da bincike da kuma ladabtar da duk wanda aka gano da hannu cikin wannan aika aika, cikinsu har da wani kamfani dake karkashin NNPC da ake zargi da hannu cikin wannan badakalar.

Ya na mai cewa ‘’ dole sai an kwashe wannan gurbataccen man da aka shigo da shi Najeriya, kafin a samu damar maye gurbinsa da ingantacce. Kuma asarar da mutane za su yi ta lalacewar motoci da dukiya har ya iya shafar lafiyarsu ba kadan ba ce idan aka ci gaba da amfani da gurbataccen man’’

Layin motoci a wani gidan mai (Tijjani Mohammed)

Masu siyar da mai a kasar dai sun kiyasta cewa kimanin lita miliyan 100 na gurbataccen man fetur aka shigo da shi Najeriya, batun da Alhaji saleh ya tabbatar, inda yace man ya wuce duk inda ake tunani idan ana batun yawansa.'’ Hakan na daya daga cikin abin da ya janyo wannan matasalar na rashin mai da layin mai da sauransu.

A bangare guda, a wani hira da muryar Amurka ta yi da shugaban NNPC Mele Kyari ya bayyana cewa ya umarci a bincika tare da rufe duk gidan man da ke da mai mai kyau kuma ya ki sayarwa, domin mafi yawa daga cikinsu na amfani da damar wajen cin riba fiye da wadda suke samu a lokutan da wannan gurbataccen man bai shigo Najeriya ba.

Batun da Alhaji Saleh ya ce dole sai hukumomin tsaro sun shiga cikin lamarin, domin tabbatar da cewa bata gari da suke boye man da sayarwa da tsada sun koma sayarwa a kan farashin da ya dace.

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da ke da wadataciyar man fetur, sai dai kawo yanzu kasar bata iya tono tare da sarrafa man da 'yan kasar ke bukata.

Saurari hirar da wakiliyarmu Shamsiyya Hamza Ibrahim ta yi Muhammad Saleh Hassan Ƙwararre a harkar man fetur a Najeriya

Your browser doesn’t support HTML5

Rashawa Na Daga Cikin Ababen Da Suka Jafa Najeriya Cikin Matsalar Man Fetur