Rasha zata kafa wani shirin kawance na yaki da ta'adaci

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha

Shugaba Vladimr Putin na kasar Rasha yace kasar sa tana son ta kafa wani shirin kawancen kasa da kasa na yaki da ta'adanci, kuma shugaban kasar Syria a shirye yake ya gudanar da zaben wakilan Majalisar dokokin kasar sa tunda wuri harma ya hada da wakilan masu hamaiya a harkokin gudanar da mulkin kasar.


Jiya Juma'a shugaba Putin ya fadawa taron habaka tattalin arzikin kasashen gabashin duniya a Vladivostic, cewa suna son su kafa wani shirin kawancen yaki da ta'adanci da kuma tsausauran ra'ayi.

Yace yanzu haka gwmnatinsa tana tuntunbar kawayenta akan wannan batu kuma yace shi da kansa ya tattauna wannan batu da takwaran aikin sa na Amirka Barack Obama ta wayan tarho.


Haka kuma shugaban na Rasha yace shugaba Recep Tayipp Erdogan na kasar Turkiya da shugabanin Saudi Arabiya da sarki Abdullah na Jordan da kuma shugaba Abdel Fatal El Sisis na kasar Masar suna daga cikin shugabanin daya tattauna wannan batu.


Shugaba Putin ya kuma ce shugaba Bashar Al Assad na Syria yayi na'am da wannan dabarar kuma a shirye yake ya gudanar da zaben wakilan Majalisar dokokin kasar sa tunda wuri, da kuma fara tuntunbar masu hamaiya da nufin hada wa dasu cikin harkokin gudanar da mulkin kasar.


Shugaba Putin yace yan gudun hijira daga Syria suna arcewa ne domin musgunawar da yan kungiyar Islamic State suke yi musu amma ba domin salon mulkin Bashar Al assad ba.


To amma gwamnitocin kasashen yammacin duniya da kungiyoyin kare hakkin jama'a sun zargin dukkansu, gwamnatin Syria da yan kungiyar Islamic state da laifin keta hakoki da yancin jama'a a kasar ta Syria.