Rasha zata kafa dogarawan yaki da ta'adanci

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Ranar Talata Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da shirin kafa dogarawan kasa da nufin yaki da ta’addanci.

Sai dai masu kula da lamura suna cewa, zai yi haka ne da nufin kwantar da hankalin al’ummar kasar yayinda yanayin matsalar tattalin arzikin kasar yake kara muni, ana kuma shirin gudanar da zabuka. Suna gani Putin ya dauki wannan matakin ne da nufin ci gaba da rike madafun iko.

A daftarin dokar dake gaban majalisa, An umarci dogarawan suyi amfani da mesar ruwa da motoci masu sulke da kayan kare kai a lokutan kwantar da tarzoma wajen tarwatsa masu zanga zanga. Yayinda daftarin ya haramta bude wuta kan wuraren dake da cunkoson jama’a ko mata masu ciki, ko nakasassu ko kananan yara. Bisa ga daftarin, Putin zai iya bada umarni kai tsaye ga dogarawan su gudanar da aikin tsaro ko kuma su bude wuta ba tare da gargadi ba idan suka fuskanci barazana.