Rasha Za Ta Ladabtar Da Wadanda Suka Yi Sanadiyar Gobarar Da Ta Kashe Mutane 64

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Gobarar da ta auku a yankin Siberia kasar Rasha ta lakume rayuka 64 yawancinsu yara lamarin da shugaban kasar ya ce ba zasu lamunta da hakan ba.

Ahalinda ake ciki kuma, shugaban na Rasha Vladimir Putin,yayi alkawarin ladabatar da duk wadanda "suka yi mummunar sakaci da ya sa gobara ta kashe mutane 64 ranar Lahadi a wata kasuwar zamani a yankin Siberia, galibin su yara ne.

Jiya Talata ne shugaban wanda ba'a juma da sake zabensa na wani sabon wa'adi ya yi wannan alkawari lokacinda ya kai ziyara inda gobarar ta yi barna abirnin Kemerovo mai masana'antu. Putin ya ajiye furanni a wurin da aka kebe domin jimami da nuna alhini ga wadanda bala'in ya rutsa da su. Daga bisani ya jagoranci wani taro, inda ya ayyana yau a zaman ranar makoki.