Wani rahoton majalisar dokokin Amurka da aka fidda yau Laraba ya zargi Rasha cewa ta dade tana kai farmaki kan tsarin dimokradiyya a ciki da wajen kasar, ya kuma yi kira akan neman hanyoyin da za’a bi na tunkarar wannan batu, abinda zai fara da shugabancin Amurka, wanda rahoton ya yi zargin cewa shugaba Trump ya gaza.
Rahoton wanda hadiman senatoci ‘yan Democrat jam’iyyar a kwamitin kula da harkokin kasashen waje suka fidda, suka kuma ba muryar Amurka kafin a gabannin sakin rahoton ga sauran jama’a, ya ce, gwamnatin shugaban Rasha Vladimir Putin ta tsara wasu matakai masu karfi wajen gwada tasirinta a aketare, da alamun kuma ta kuduri anniyar amfani da kusan duk wata hanya don ganin ta gurgunta gwamnatocin dimokradiyya da kuma kawancen su.
Sakamakon bincke na tsawon watanni da kuma musayar bayanai da gwamnatocin kasashen waje da Rasha ke fako, rahoton mai shafi 206 ya bada cikakken bayani akan yadda Rasha ta yi amfani da karfin ikon ta a wasu kasashe.