Rasha Ta Yi Bukin Cin Jamus Da Yaki Kadaran-Kadahan

  • Ibrahim Garba

Babu kowa a dandalin Red Square sai 'yan sanda

Jiya Asabar kasar Rasha ta yi bukin zango na 75 na zagayowar ranar da ta yi galaba kan kasar Jamus da ke karkashin mulkin Nazi lokacin ita kuma Rashar ke Tarayyar Soviet (Sobiyet). To amma saboda dada tabarbarewa da matsalar cutar corona ke yi a kasar, ala tilas aka kauce ma yin bukukuwan da aka saba.

Jami’ai a kasar ta Rasha, jiya Asabar sun bayyana sabbin kamuwa da cutar ta COVID-19 su wajen fiye da 10,000 cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, wanda ya sa jimlar wadanda su ka kamu da cutar ya cilla zuwa 200,000. Rasha ta yi ta bayyana masu kamuwa da cutar wajen fiye da 10,000 kulluyaumin a wannan satin, wanda ya zarce na Faransa da Jamus, inda ta zama ta biyar a jerin kasashe mafiya masu dauke da cutar a duniya.

An soke Faretin Ranar Nasara wanda akan yi a babban dandanlin birnin Moscow (Masko), to amma a kasar Belarus mai makwabtaka da Rashar an yi wani gagarumin faretin Ranar Nasara Minsk, wanda ya tara dubban sojoji masu maci da kuma ‘yan kallo.

Shugaban Belarus Alexander Lukashenko ya dage sai da aka yi faretin duk da cewa a kasar ce cutar ta fi yaduwa a fadin gabashin Turai, bisa ga alkaluman Jami’ar John’s Hopkins.