Rasha Ta Nuna Sha'awar Maye Gurbin Amurka A Hukumar Kare Hakkin Bil Adama Ta Duniya

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Rasha ba ta bata lokaci ba wajen bukatar hanzarin maye gurbin Amurka a Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya.

Rasha ba ta bata lokaci ba wajen yin hanzarin maye gurbin Amurka a cikin Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta MDD wacce Amurka din ta fice daga cikinta, inda nan take Rasha ta bayyana sha’awarta na darewa kan kujerar, tana kuma nuna cewa Amurka ba ruwanta da harakar kare hakkin Bil Adama.

Su ma jami’an diflomasiyyar Turai, hade da kafofin watsa labaran Rashar, duk sun yo caaa wajen nuna ita gwamnatin ta Rasha a matsayin mai kare hakkokin Bil Adama, kuma suna nuna cewa janyewar Amurka kamar juya baya ne ga wahalhalun da al’ummar duniya ke fuskanta a sanadin taka hakkokinsu da ake yi.