Rasha Ta Kama Wani Ba’Amurke A Birnin Kan Zargin Leken Asiri

  • Ibrahim Garba

Shugaba Bladimir Futin (Vladimir Putin)

Jami’an Hukumar Tsaron Tarayya ta Rasha (FSB) sun fitar da wata takardar bayani a yau dinnan Litini, ta kama wani ba’Amurke a birnin Masko (Moscow) kan zargin leken asiri.

Kasar Rasha ta kama wani ba’Amurke a birnin Moscow kan zargin leken asiri, a cewar gidan talabijin din gwamnati.

Jami’an Hukumar Tsaron Tarayya ta Rasha (FSB) sun fitar da wata takardar bayani a yau dinnan Litini, mai cewa tun ranar 28 ga wannan wata na Disamba aka kama ba-Amurken mai suna Paul Whelan yayin da ya ke take-taken leken asiri, kuma an fara binciken wannan laifin.

Ba su bayar da karin bayani ba, to amma kamfanin dillancin labaran Rasha na TASS ya ce Whelan zai fuskanci fursunan tsawon shekaru 20 muddun aka same shi da laifi.

Nan take dai jami’an gwamnatin Amurka ba su ce komai ba.

Wannan kamun na faruwa ne a daidai lokacin da zarge-zargen leken asiri ke dada sukurkuta dangantaka tsakanin Rasha da yammacin duniya, ciki har da batun sa guba ma wani tsohon jami’in leken asirin Rasha da diyarsa a Burtaniya, da kuma samun wata ‘yar Rasha da laifin leken asiri a Amurka.