A yau Asabar Fadar Kremlin ta fitar da wata sanarwa, tana mai jaddada aniyarta, ta ganin an tabbatar da zaman lafiya, ta hanyar kawar da ‘yan ta’adda, wanda hakan a cewarta zai kawar ‘yan ta’adda kasar ta Syria.
A jiya juma’a, Amurka da Rasha suka kaddamar da wata tattaunawa kan yadda za a cimma matsayar tsagaita wuta a kasar ta Syria.
Jami’an gwamnatocin biyu, sun tattauna ne a Geneva domin samar da hanyar da za a samu dogon lokaci na tsagaita wuta, saboda akai kayan agaji ga yankunan da aka yiwa kawanya.
Kasashe 17 da ke marawa gwamnatin Syria baya, sun amince da kafa wani kwamiti da zai maida hankali wajen ganin an cimma matsayar tsagaita wutar a karkashin kulawar Majalisar Dinmkin Duniya, a taron da suka yi a Munich, inda aka nada Amurka da Rasha a matsayin wadanda za su jagorancin tafiyar.