Rasha Ta Hau Kujerar Naki Akan Kawarta Syria, a Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Amurka ta sake gabatar da kudurin neman a gudanar da bincike kan Syria dangane da yin anfani da makamai masu guba akan al'ummarta jiya Alhamis a Majalisar Dinkin Duniya, amma Rasha, mai goyon bayan Syria, ta hau kujerar naki

A jiya Alhamis Rasha ta hau kujerar na-ki, yayin jefa kuri’a kan wani kuduri da Amurka ta gabatar a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya nemi a tsawaita binciken kasa da kasa da ake yi akan zargin da ake yi wa Syria na yin amfani da makamai masu guba.

Sa’oi bayan haka kuma, kwamitin ya yi watsi da wani kuduri na daban da Rasha ta gabatar, bayan da ya gaza samun kuri’u tara, wadanda sune adadi mafi kankanta da ake bukata kafin a amince da shi.

Daga cikin bukatun da Rashan ta gabatar a kudirin, har da neman a yi sauyi ga wadanda aka daurawa alhakin aikin wanda Amurka ke adawa da hakan.

Wannan shine karo na goma da Rashan ta ke hawa kujerar na-ki kan kudirin na Syria.

Hakan kuma na nufin, tun da kudirin bai samu karbuwa ba, aikin da aka dorawa masu binciken zargin da ake wa Syria na amfani da makamai masu guba, ya kawo karshe Kenan a tsakar daren jiya Alhamis.

A jiya Alhamis din, Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta ce kin amincewa da kudurin “babban koma baya ne.”