Rasha ta yi amfani da karfin ikonta na hawa kujerar-na-ki a jiya Talata a Majalisar Dinkin Duniya, inda ta dakile wani yunkuri na tsawaita ikon da aka bai wa masu bincike harin makami mai guba da aka kai a Syria.
A lokacin kada kuri’ar da kwamitin sulhun na Majalisar Duniya ya yi, kasashe 11 sun amince a tsawaita wa’adin masu binciken zuwa shekara daya, yayin da Rasha da Bolivia suka ki amincewa da wannan mataki, sannan China da Kazakstan suka hau kujerar ‘yan-ba-ruwanmu.
A gobe Alhamis ake sa ran tawagar masu binciken za za ta bayyana rahotonta a baina jama’a, wanda ake sa ran zai fayyace wanda ke da alhakin kai hari da makami mai guba a ranar 4 ga watan Afrilu a garin Khan Sheikhoun da ke hannun ‘yan tawaye a kudancin Idlib, wanda ya halaka tare da jikkata fararen hula da dama.
Kwanaki uku bayan wannan lamari, Amurka ta kai harin sama a wani filin tashin jiragen soji na Syria, bayan da Washington ta zargi gwamnatin shugaba Bashar al’ Assad da kai harin wanda ke dauke da iskar gas mai cike da guba.