Kasar Rasha tace ta samo bayanai daga na'urar daukar magana da aka gano daga jirgin yakin kasar da Turkiyya ta harbo cikin watan jiya.
WASHINGTON DC —
Shugaban hukumar kula lafiyar zirga zirgan jiragen yakin kasar Sergei Bainetov, yace bincike da suka gudanar kan na'urar ya nuna cewa 13 cikin 16 kwakwalwar na'urar duk sun gama yawo sakamakon harbin,saura ukun kuma sun sami lahani.
Duk da haka Sergei yace kawararru zasu yi aiki domin fito da bayanai daga cikinsu, sai dai aikin zai dauki lokaci.
Turkiyya ta harbo jirgin yakin na Rashan samfurin SU-24 ranar 24 ga watan Nuwamba kusa da kan iyakarta da Syria, tana zargin jirgin ya keta sararin samaniyarta.