Rasha na Zargin NATO da Makarkashiya

Wakilin Rasha a NATO, Alexander Grushko

To fa kasar Rasha na zargin rundunar kawance ta NATO da yin tunani kamar na lokacin zaman gabar akida, wanda aka taba yi tsakanin NATO da Rasha a baya, saboda NATO ta dakatar da hada kai da Rasha saboda kwace yankin Kirimiya ta tayi daga hannun kasar Ukraine.

Jakadan Rasha a NATO, Alexander Grushko ya rubuta akan shafinsa na Twitter cewa ‘NATO ta farfado da halayenta na lokacin zaman gabar akida’.
Ministocin harkokin wajen NATO, suna ci gaba da tattauna a birnin Brussels dake kasar Belgium yau laraba akan takkadamar Ukraine din.

Jiya Talata ministocin, a hukumance suka yanke shawarar dakatar da duk wata mu’amalar soji da fararen hula da Rasha. Ministocin sunce basu amince da hada yankin Kirimiya mallakar Ukraine da Rasha ba, kuma sun yi kira ga Rasha akan tayi maza-maza da bi dokokin kasa da kasa.

Ya zuwa yanzu Hanyoyin diflomasiyya a bude suke tsakanin NATO da Rasha.