A yau Litinin Gwamnatin Rasha ta bayyana damuwarta game da kudurin Shugaban Amurka Donal Trump, na ficewa daga wata muhimmiyar yarjejeniyar makamai da aka kulla a zamanin yakin cacar-baka wato "Cold War"a turance.
Ta kara da cewa wannan matakin da Amurkan ke so ta dauka ka iya jefa duniya cikin yanayi mai hadari.
Dmitry Peskov, mai magana da yawun Fadar Shugaban Rasha ya fadawa manema labarai cewa, Rasha ba ta karya ka’idojin yarjejeniyar ba, yana mai cewa idan Amurkan ta ce za ta soma kera wasu sababbin makamai masu linzami, ya zama wajibi Rasha ita ma ta shiga kera nata makaman sababbi.
Peskov ya ce jami’an kasarsa suna so su samu karin bayanai akan shirye-shiryen da Amurka ta ke yi game da yarjejeniyar kayyade makamai masu karamin karfi da ke tafiyar karamin zango, a lokacin tattaunawar da za su yi cikin wannan makon da mai bai wa shugaban Amurka shawara akan harkokin tsaro John Bolton.
A yau Litinin Bolton zai gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da kuma shugaba Vladimir Putin.