Rasha Na Cigaba da Taimakawa Shugaban Syria al-Assad

Samfarin jiragen yakin da Rasha ke anfani dasu cikin Syria

Gwamnatin Rasha a karkashin Putin na yakar 'yan tawaye da zummar tabbatar da ganin gwamnatin Bashir al-Assad ta rayu

Rasha ta sake kai sabbin hare hareda jiragen sama akan sansanin 'yan tawayen Syria jiya Lahadi a kokarin da kasar ke na taimakawa shugaba Bashar Al-Assada ta sake kwato wuraren da 'yan tawaye suka karbe.

Rasha ta hakikance cewa yawancin wuraren suna Tal Skik ne wani wuri dake cikin tsaunuka a yankin Idlib da ya dade yana karkashin ikon 'yan tawaye..

Saidai Rasha ta cigaba da ikirarin cewa yankin na karkashin 'yan ta'adan ISIS ne. Amma a hakikanin gaskiya wuraren da Rasha ta auna hare haren da ta kai wurare ne dake karkashin ikon wasu 'yan tawayen dake yaki da gwamnatin Assad..

A wata fira da ya yi da wani gidan talibijan na kasar Rasha shugaba Vladimir Putin ya kare manufar tsoma bakin Rasha cikin rikicin na Syria. Manufar itace taimakawa gwamnatin Syria ta samu ta tsaya bayan hakan shugaban ya nemi sasantawa ta hanyar siyasa .

To saida shugaban Amurka Barack Obama a firar da ya yi da gidan talibijan CBS cikin shirin nan nasu da ake kira 60 Minutes jiya Lahadi yace shigar Rasha cikin rikicin Syria ba domin wani abu ba ne illa kare gwamnatin Assad..

Dama can Syria ita ce kasa daya tilo da tale da kawance da Rasha a Gabas ta Tsakiya. Barack Obama yace shi ya sa yau maimakon ta kare sansaninta a Syria yanzu Putin ya shiga yakin gadan gadantare da yin nfani da sojojinsa domin gwamnatin Assad ta rayu