Rasha tace zata kara tsawon lokacin da zata ci gaba da daina kai hare-haren jiragen sama akan birnin Aleppo na tsakiyar kasar Syria, inda tace su ma sojojin kasar dake biyayya ga shugaba Bashar al-Assad sun dauki irin wannan matsayin na jan burki daga kai hare-hare akan yankunan ‘yan tawayen kasar.
WASHINGTON, DC —
Wani hafsan sojan Rasha, Lt. Gen. Sergei Rudskoi, wanda ya bada sanarwar, yace mayakansu da na Syria sun kai mako daya suna zaune a wani wuri kamar kilomita 10 wajen birnin na Aleppo.
Sai dai kuma wannan sanarwar da Rasha ta bayar, ba’a tabattar da gaskiyarta ba, kuma bisa ga dukkan alamu, ta sha banban da abubuwan da ake ji suna fitowa daga kungiyar ‘yan adawan Syria na “Observatory” wacce tace tun ranar Assabar da ta wuce aka koma ga ci gaban kai farmaki akan Aleppo, watau bayan sa’oi ukku da zuwa karshen yarjejeniyar tsagaita wutan da aka kulla.