Rasha Da China Sun Ki Amincewa Da Kakabawa Siriya Takunkumi

Jiya Talata da Rasha da China sun hau kujerar na ki don taka burki ma wani yinkuri a Kwamitin Sulhun MDD na kakaba ma gwamnatin Siriya takunkumi saboda amfani da makamin guba kan jama'arta.

Wannan karo na bakwai kenan a tsawon shekaru kusan shida na yakin Siriya da Rasha ta yi amfani da ikonta na hawa kujerar na ki don kare gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

Kasar Bolivia ma wacce mamba ce ta Kwamitin Sulhun, ita ma ta kada kuri'ar adawa da matakin. Kasashen Masar da Habasha da Kazakhstan kuwa sun kaurace ma kuri'ar. To amma har an samu adadin kuri'o'in da ake bukata don aiwatar da takunkumin, idan da ba don hawa kujerar na kin da kasashe biyu masu kujerar dindindin a Majalisar ba, wato Rasha da China.

Daftarin kudurin da bai samu nasara ba, ya tanaji kakaba takunkumi ga gwamnatin Assad saboda amfani da makamin guba a akalla wasu hare-hare uku da aka kai kan farar hula a 2014 da kuma 2015.