Shugaban Amurka Mai jiran gado Donald Trump ya yi amfani da kafar da ya saba amfani da ita wajen mika sakonsa ga jama'a, wato Twitter, wajen yin watsi da wani rahoto mai nuna cewa kasar Rasha ta tattara wasu bayanai da su ka shafi tabargazarsa da zummar tilasta shi ya yi yadda su ke so nan gaba.
"Wannan kagaggen labari ne, kuma bita da kullin siyasa ne," a cewar Trump ta kafar Twitter a rubutun da ya yi da manyan haruffa da yammacin jiya Talata bayan bullar rahoton. Ko da safiyar yau Laraba, Trump ya cigaba da mai da martani, ya na mai kafa hujja da karyatawar da Rasha ta yi cewa ta na da wani bayani kan tabargazarsa, ya kara jaddada cewa, "Rasha ba ta taba yinkurin amfani da ni ba."
Rahotannin kafafen yada labarai sun nuna cewa wani bayanin da jami'an leken asirin Amurka su ka harhada ya kunshi wani sashi mai nuna cewa jami'an yakin neman zaben Trump sun hada kai da jami'an leken asirin Rasha. An ce sashin ya kuma tabo batsa da Trump ya tafka.