Albarkacin ranar yaki da cin hanci da rashawa wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware, Majalisar Dokokin kasar Nijar ta shirya taron horo wanda ya hada da ‘yan Majalisa da jami’an tsaro, domin fadakar da su game da irin rawa da ya kamata su taka wajen magance wannan matsala.
Cin hanci dai wani al’amari ne da akayi amannar cewa a ‘yan shekarun nan yana kokarin kafuwa da gindinsa a kasashen duniya baki daya, kuma bayanai na nuni da cewar kasar Nijar ma bata tsira ba bisa la’akari da yadda karbar na Goro ke zama wata sabuwar al’ada a gurin Jami’ai, wasu lokutan har a gurin talakawa.
Duk da yake hukumomin Nijar sun kafa hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa, amma kasar na daga cikin jerin kasashen da ke samun koma baya sanadiyar cin hanci da rashawa.
Bincike ya nuna cewa fannin siyasa na kan gaba a jerin fannonin da cin hanci yafi kamari, inda ake zargin ‘yan siysa da amfani da kudi domin samun yardar talakawa ‘dabi’ar da sakatare janal na kungiyar ANLC Mamane Wada, ke ganin akwai bukatar hanzarta murkushewa.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Mumuni Barma daga Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5