Sanata Hadi Sirika yace suna da hujja babba na sake gina filin dake zama na kan gaba a harkar tsahi da saukan jirage na kasa da na kasashen waje.
Yace tsawon kilomita ukku ne da digo shida za'a gyara cikin makwanni shida kafin a sake bude filin. Gyaran zai ci kudi fiye da Nera biliyan biyar.
Dangane da jiragen kasashen waje ya musanta zargin cewa ma'aikatarsa basu yi taro da su ba. Hadi Sirika yace sun yi taro dasu ba iyaka. Sun ziyarci ofisoshin jakadancin da lamarin ya shafa inda suka yi cikakken bayani.
Yace akwai kasashen da suka ce zasu dinga zuwa suna sauka a Kaduna kamar yadda aka tanada. Jirgin kasar Turkiya da na Jamus da dai sauransu sun yi alkawarin sauka a Kaduna.
Gwamnatin Najeriya tace ta kammala shirin tsaro a sabon filin jirgin sama na Kaduna wanda aka yi masa gyara domin maye gurbin na Abuja cikin makwanni shidan da za'a yi ana gyara, inji babban sifeton 'yansandan Najeriya Ibrahim Idris.
A cewarsa yace sun baza 'yansanda da dama akan hanyar Kaduna zuwa Abuja tare da yin anfani da jirgi mai saukar angulu.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5