A jiyane a fadin duniya aka gudanar da bukukuwan ranar nakasassu na duniya, na wannan shekarar majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 3 ga watan Disambar kowace shekara ta kasance ranar bukin mutane masu dauke da nakasa a sassan jikinsu.
A jawabin daya gabatar dangane da bukin ranar nakasassu na wannan shekarar, babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr.Antonio Gueteres, ya shaida cewa akwai mutane fiye da miliyan 100,000,000 da suke dauke da nakasa iri daban-daban ajikinsu.
Mr. Antonio Gueteres ya bayyana cewar, masu dauke da nakasa kan kasance cikin yanayi na kadaita a sanadiyar gujewar da al’umma kemusu. Suna kuma fuskantar nuna ban banci, da kuma kyama daga wurin jama’a.
A dangane da hakane cikin alkawarin ajandar shekara ta 2030, yayi batun cewa baza'a bar wani a baya ba wajen kawo dai-daito, da inganta matsayin rayuwa, arziki da kuma harkokin siyasa, domin a rinka damawa da mutane masu nakasa a dukkan kasashen duniya.
Kamar yadda yake kunshe a daftarin kundin dokar Majalisar Dinkin Duniya dake batu kan damar da masu nakasa ke dashi.
Taken bukin ranar nakasassu a wannan shekara shine “Inganta nakasasshe da tabbatar da tarraya don kawo daidaito."
Your browser doesn’t support HTML5