Ranar Matasa na Duniya na Shekarar 2015

  • VOA Hausa

IYD2015 Buhari

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin inganta rayuwar matasa, a fannonin da suka shafi ilimi da samar da ayyukan yi damagance matsalar yunwa da talauci da samar da kariya daga kamuwada cutar AIDS ko kuma SIDA tare da al’amuran da suka shafi manya da matasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a Abuja, babban birnin Najeriya, kuma ya jaddada rawar da matasa kan taka wajen tabbatar da amintacciyar gwamnati.

Matsalar rashin aikin yi na daya daga cikin manyan matsalolin da keaddabar Najeriya, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin magance wannan matsala da kuma inganta rayuwar matasan Najeriya.

Miliyan 60 a cikin miliyan 180 na al’umar Najeriya, matasa ne, kuma kashi hamsin daga cikinsu, na fama da rashin aikin yi saboda rashin gwaninta da kwarewa da ma cancanta.

Tambayar mu ta yau ita ce:

Ku cigaba da bin wannan maudu'in a shafin Twitter tare da #IYDNG2015