Ranar Marubuta ma Ilmanta a Al'umah

Ranar Marubuta a Duniya

Baiwar rubutu wani abune da yakamata ace kowane mutun yayi amfani da tashi baiwar wajen ilmantarwa, nishadantarwa da kuma fadakarwa. Malam, Zahradeen Ibrahim Kallah, wani marubucin kirkira ne kuma me rajin kare hakkin marubuta, ya nuna damuwar su dangane da yadda wasu mutane ke amfani da wata dama da suke da ita wajen dan-kwafar musu da sana’a, mafi akasarin mutane sukan wallafa littafai da suka rubuta da irin basirar da Allah yayi musu wajen ilmantarwa da ma nishadantarwa, wanda ta haka mutane da dama kan anfana da wannan rubuce rubucen a fanoni da dama.

Amma wani abu damuwa anan shine, wasu mutane kuma na amfani da wannan dammar wajen gurza wadannan littatafai da wasu marubuta ko masana su ka wallafa batare da sannin ko izininsu ba, ko kuma akansamu wasu na bada hayar wadannan littatafai wanda duk batare da sanin wadannan marubutan ba.

Wannan wata dabi’a ce wadda a zahirin gaskiya bata da wata makoma illa maida wannan sana’ar ta rubuce rubuce baya. Mafi akasarin wadannada ke wannan rubuce rubucen kan ji wani iri idan suka ga ana musu wasa da sana’a, wanda wanna yasa wasu ma suna kokarin barin wannan harkar ta rubuce rubucen, a gaskiya wannan ba karamin nakasu bane ga sana’ar rubutun kirkira ba.

A wanna yanayi yakamata al’uma suyi la’akari da irin gudunmawar da wadannan marubutan ke badawa don haka a guji wannan dabi’ar ta satar basira, don idan suma sauran al’uma zasu sa kansu cikin irin wannan sana’ar to zaka ga cewar ansamu yawaitar masu irin wannan basirar, kuma ta haka za’asamu yawan masu ilimi da hazaka.