Shekaru goma ke nan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudurin da ta ayyana ranar 20 ga Maris na kowace shekara, a matsayin ranar farin ciki ta duniya.
An kebe ranar ce domin jaddada muhimmancin farin ciki da jin dadin jama’a baki daya.
A rahoton Farin Ciki na Duniya na 2023 da ya fito yau Litinin, Kasar Ghana na matsayi na 107 cikin kasashe 137 da aka yi nazarin mutane kimanin 100,000. Kasar Finland ce ta kasance ta daya, karo na shida a jere a duniya, yayin da kasar Mauritius ta zo ta daya a Afirka.
Majalisar Dinkin Duniya ta fara bikin ne a shekarar 2013, kuma taken bikin wannan shekarar 2023 shi ne: “A yi La’akkari. A yi Godiya. A yi Kirki.
Dakta Nasiba Tahir, Malamar Ilmin Kwakwalwa da halayyar dan Adam a jami’ar Islama ta Ghana, ta ce majalisar dinkin duniya (MDD) ta ware wannan rana ne domin farin ciki shi ne yake karawa mutane kwarin gwuiwar gudanar da aikin da zai sa kasa ta ci gaba.
Dakta Nasiba ta kara da cewa, burin MDD a samu daidaito wajen karawa jama’a farin ciki ba tare da nuna banbanci ba, ta hanyoyi uku da taken bukin bana ya yi nuni.
Rahoton Farin Ciki na Duniya karo na 10, wanda aka buga yau Litinin, domin ya zo daidai da ranar farin ciki ta duniya, ya yi nazari kan mutane sama da 100,000, kuma ya gano kasar Finland ta kasance kasa mafi farin ciki a shekara ta shida a jere.
Amurka ta kasance kasa ta 15 mafi farin ciki a duniya. Daga cikin kasashen 20 na farko, 15 daga cikinsu kasashen Turai ne. A kasan jerin sunayen, kasar Afghanistan ce matsayi na 137, sai Lebanon tana matsayi na 136.
Kasashe 13 daga cikin 20 mafi ƙarancin farin ciki sun kasance a Afirka ne, inda kasar Sierra leone ta kasance kasar Afirka ta karshe, kuma ta 135 a duniya. Kasar Najeriya ce ta 95 a duniya; sai Kamaru na bayanta a matsayi na 96; kasar Ghana tana matsayi na 107; Kasar Nijar na bayan Ghana a matsayi na 109
Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako daga Accra:
Your browser doesn’t support HTML5