Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan ra nace da za ake amfani da ita wajen wayar da kan al’umma game da abubuwan da ke tauye ‘yancin ‘yan jarida. Tare da nuna yadda shekaru aru-aru ake jawa ‘yan jarida burki ta hanyar cin tara, kai hari ko dauri a kurkuku, ko kisa.
Taken taron shekarar nan shine ‘Bayyano Cin Zarafin Aikin Jarida a Fadin Duniya’. Kasar Finland sun wuce kowa a yin bikin wannan rana don sun shekara 5 suna yinsa a jere ba fashi, a inda kasashen Norway da Denmark ke biye da ita. Kasar Birtaniya ce ta 34, Amurka ta 49 sai kuma Japan ta 61.
Kasar Afghanistan ce 122 da Zimbabwe ta 131, sai Cuba ta 169 da kuma kasar Sin a mataki na 176. Koma baya a wannan lissafi sune Turkmenistan (Tokmenistan), Korea ta Arewa da Eritria da suka fado a rukunin lamba ta 180.