Ramuwar Azumi Akan Wanda Bai Fara Da Jama'a Ba Bayan Ganin Watan Ramadan

wanda bai tashi da azumin gama gari ba zai rama daya bayan sallah

Sheikh Useini Zakariyyah Na Masallacin Usman Bin Affan na Abuja ya ce ana so a rama azumin daga an gama bikin Sallah

Babban Editan Sashen Hausa Aliyu Mustpha ya tattauna da Sheikh Useini Zakariyyah na Masallacin Usman Bin Affan na Abuja akan wasu mahimman batutuwa masu nasaba da azumi.

Da farko Sheikh Useini Zakariyyah ya fara ne da yin karin haske akan sharadin ramuwar azumi, musamman ma ramuwa ga wanda ya sha azumin ranar farko saboda bai san an ga wata ba.

Your browser doesn’t support HTML5

me shari'a ta ce kan ramuwar azumi da fara azumi a wata kasa.- 4':39"

Haka nan kuma a cikin tattaunawar ta su da Aliyu Mustapha, Sheikh Useini Zakariyyah yayi karin haske game da yadda mazauna wasu kasashen waje ke bin ganin watan azumi a kasashen su, su fara azumi ko da kuwa ba a ga wata ba a kasar da suke da zama.