Jam’iyya mai mulki ta Afrika ta kudu wato ANC ta zabi Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugabanta.
Yanzu tamkar ana kallon Ramaphosa a matsayin wanda zai iya zama shugaban Afirka ta Kudu, idan aka yi zaben shugaban kasa a shekarar 2019.
Ya kayar da tsohuwar minista Nkosazana Dlamini Zuma.
Kusan mambobi 5,000 ne suka yi zaben wanda aka gudanar a Birnin Johannesburg.
Ramaphosa zai maye gurbin shugaban kasar ta Afirka ta kudu wanda zai sauka daga kujerar shugabancin jam'iyyar saboda zargin cin hanci da rashawa da ya dabaibaye shi.
Amma zai ci gaba da zama a matsayinsa na shugaban kasa har zuwa shekarar 2019 da za a yi zabe.
Jam'iyyar ta ANC ta saba lashe kusan dukkan zabukan da aka yi tun bayan da aka kawo karshen mulkin turawa marasa rinjaye a shekarar 1994.