Yayin da aka fara azumin watan Ramadana a Jamhuriyar Nijar da sauran sassan duniya, kiristoci a birnin N'Konni sun yi wa musulmi fatan alheri albarkacin soma azumin na bana.
"Muna muku fatan alheri 'yan uwanmu, iyayenmu, kannenmu da matanmu da suka fara wannan azumi na watan Ramadana." Inji shugaban kiristoci na birnin N'Konni, Pastor Abubakar Musa.
A na su bangaren, musulmi sun nuna jin dadinsu da wannan kulawar ta kiristoci a irin wannan lokaci.
"Da ma wannan ba bakon abu ba ne, a zamanin Manzon Allah ya zauna da kiristoci, ya zauna ma da wadanda ba su da addini." In ji Malam Mahamadu Dan Wazifa
Baya ga fatan alherin, kiristocin har ila yau, sun ja hankulan 'yan kasuwa da su sassauta farashin kayayyakin masarufi.
"Gaskiya muna kira ga 'yan kasuwa a cikin wannan lokaci na azumi, muna azumi ne domin neman lada, saboda haka, mu tausaya wa mutane, domin wani lokaci idan ana azumi kaya kan yi tsada." Inji Pastor Musa.
A kowane lokaci musulmi da kirista sukan wa junan barka a lokutan salloli ko azumin juna a Nijar, abin da ke tabbatar da kyakkyawar dangantaka da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.
Your browser doesn’t support HTML5