Hankulan manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya, ya fara karkata kan dan wasan tsakiya na Barcelona Philippe Coutinho, wadda suka hada da Chelsea, Paris-saint German, da kuma Manchester United.
Dan wasan wanda ya koma Barcelona daga Liverpool a farkon shekarar 2018, a kan kudi fam miliyan 142, an masa tsammanin zai zama daga cikin jagororin yan wasan kungiyar, inda a ke ganin cewar shi ne zai maye mata gurbin dan wasanta Iniesta.
Amma kuma, sai dai zuwan dan wasan Barcelona ke da wuya sai aka maidashi dan wasan gefe wanda hakan ya sa ya ke takara da Damebele, wadda yafi Countinho gudu da iya takaleda a bangaren gefe. Wannan ya janyo masa matsala ta rashin samun gurin shiga wasa akai akai.
Wata majiya da ke kusa da Coutinho, ta ce tuni dan wasan ya shaida wa takwarorin sa a Barcelona ce wa, ya na sa ran rabuwa da kungiyar ta sa a karshen kakar wasa ta bana.
Kungiyar Manchester United ita ce kungiyar da a ka fi alakantawa da daukar Coutinho tuntuni
Sai dai ita ma kungiyar Chelsea ta ce a shirye ta ke ta biya euro miliyan €142, wajen sayen Philippe Coutinho daga Barcelona, domin ya maye gurbin
dan wasan ta Eden Hazard wadda Real Madrid ta ke yunkurin daukar sa a kakar wasa mai zuwa.
Rahotanni sun ce, Chelsea na fatan sayen Coutinho ne, da kudaden da Real Madrid za ta sayar dan wasanta Eden Hazard, cinikin da a ke sa ran zai tabbata a karshen kakar wasa ta bana.